Mai magana da yawun shugaba Buhari Femi Adesina ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa shugaba Buhari ya sake tafiya London ne domin ya ga likitocinsa a kan rashin lafiyarsa, kuma a cewarsa babu wani abin damuwa dangane yanayin nasa.
Adesin bai yi karin haske a kan lokacin da shugaba Buhari zai dawo Najeriya ba, amma dai ya tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasar Farfesa Osinbajo ne zai ci gaba da mulkin kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasa, kuma tuni Buhari ya aike wa majalisar dattijai da wasika da ke sanar da su hakan.
Shugaba Buhari dai ya dauki tsawon kwanaki ba a gan shi ba, lamarin da ya jawo magnganu masu karo da juna a tsakanin 'yan kasa, amma a ranar Juma'a da ta gabata shugaban ya halarci sallar Juma'a a cikin masalalcin da ke fadarsa, bayan kammmala sallar kuma ya koma cikin gida, a jiya kuma ya gana da 'yan matan Chibok 82 da aka yi musayarsu da mayakan Boko Haram.